Abin Da Ya Sa ’Yan Sanda Suke Kama Mutanen Da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba
Manage episode 457259731 series 3311743
Lokacin bukukuwa lokaci ne da ake samun karuwar zirga-zirga da hada-hadar jama’a.
Wannan ne ya sa hukumomin da nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansu suke kara kaimi wajen ganin sun tabbatar da doka da oda.
Sai dai wasu ’yan Najeriya sukan yi zargin cewa ’yan sanda kan yi amfani da wannan dama don kamen mutane babu gaira babu dalili.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba ne kan sahihancin wannan zargi.
717 episodes